29 Yuli 2019 - 04:00
Tunisia : An Yi Jana’izar Béji Caïd Essebsi

A Tunisia a jiya Asabar ne akayi jana’izar shugaban kasar Béji Caïd Essebsi, wanda Allah, ya yi wa rasuwa a ranar Alhamis data gabata, yana mai shekaru 92 a duniya.

(ABNA24.com) A Tunisia a jiya Asabar ne akayi jana’izar shugaban kasar Béji Caïd Essebsi, wanda Allah, ya yi wa rasuwa a ranar Alhamis data gabata, yana mai shekaru 92 a duniya.

Daga cikin wadanda suka halarci jana’izar, har da shugaban kasar faransa, Emanuel Macron, da shugaban Palasdinawa Mahmud Abass, da shugaban gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya Faez Al’Saraj, da sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani.

An dai yi jana’izar ce tare da halatar iyalen mirigayin, da girmamawa ta sojoji gaban dimbin al’ummar kasar ta Tunisia.

Mirigayi Béji Caïd Essebsi, shi ne wani shugaban kasa na farko a Tunisia da aka zaba ta hanyar demokuradiyya, bayan guguwar neman sauyi ta 2011 data yi awan gaba da mulkin Ben Ali.



/129